<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>244</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Yesu Mai Cetona, ga ni nan a giciyenka.
 Ina neman ceto dai, ceto daga zunubi.

[V2]
 KORUS
 Na dogara gare ka, Almasihu Ɗan Allah.
 Kai kaɗai Mai Ceto ne, kai ka mutu domina.

[V3]
 2) Kai ne ka san zamana, kai kuwa ka san tashina
 Cikin dukan aikina da tunanin zuciyata.
 Korus

[V4]
 3) Kai ne ka ke kiwona, kai ne Makiyayina.
 Cikin wannan duniya, kiyaye ni lafiya.
 Korus

[V5]
 4) Almasihu Masoyi, zauna cikin zuciyata,
 Cika ni da ƙaunarka, bar in bi ka, kai kaɗai.
 Korus</lyrics>
<title>Ya Yesu Mai Cetona, Ga Ni Nan A Giciyenka LW244</title>
</song>